AN HANA WASAN TASHE A KANO


Tashe wasannin al`ada ne da ake yi a cikin watan azumi, musamman ma daga goma sha biyar ga wata; inda maza da mata, yara da matasa ke bin gida-gida domin yin wasan tashe, don debe kewa ga masu azumi a duk shekara.

Sai dai, a bana mahukunta a Kano sun hana yin wasan tashe saboda dalilai na tsaro, lamarin da ya rage armashin hidimomin da ake yi a cikin watan azumin.


Like it? Share with your friends!

-3
44 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like