An gudanar da zanga zanga a Batsari ta jihar Katsina


Yanzu haka al’ummar karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina suka gudanar da zanga-zangar lumana domin jawo hankalin gwamnatoci, sakamakon irin kisan kiyashin da ake yi musu tare da kone kauyun Wagini da mahara suka yi, lamarin da ya yi sanadiyyar raba dubban mutane da muhallin su da yin hijira zuwa wasu yankuna.

Kuma sun koka akan irin rashin ko’in kula da mahakunta ke nuna musu duba da barazana da rasa rayukan al’umma da ake fama da shi ba bu dare ba bu rana, wanda hatta ragowar makofan su irin su D’antudu, Garin Yara, Malabo lamarin bai barsu ba ciki har da Sabon Garin Gamji da ke yankin karamar hukumar Safana inda suka ka karbi dubban ‘yan gudun hijira wanda suma yanzu haka a tsaye suke kwana saboda tsoron zuwan maharan, inda suka bayayyana cewar suna rokon gwamnatin tarayya data jiha da su dubi girman Allah da irin rayukan da ke salwanta su kawo musu daukin gaggawa.


Like it? Share with your friends!

-3
71 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like