An Gudanar Da Gagarumin Taron Taya Ganduje Murnar Cin Zabe A Kano


Cibiyar kafar sadarwar zamani ta Shugaban kasa, Muhammadu Buhari [BNMC] reshen Jihar Kano, karkashin jagorancin shugabanta, Bashir Abdullahi Elbash, hadin gwiwa da kungiyar [Zero Tension] a jiya sun gudanar da liyafar cin abincin dare domin taya mai girma gwamnan Jahar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar samun nasarar lashe zabe a karo na biyu.

Taron wanda ya gudana a babban dakin taro na [Tahir Guest Place]. Ya kuma samu halartar manyan baki wadanda su ka hada da:

1. Mai girma tsohon gwamnan Kano, kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano).

2. Mai girma mataimakin Gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya samu wakilci.

3. Mai girma Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas (Dan Sarki Jikan Sarki). Wanda ya samu wakilci.

4. Malam Bashir Ahmad, mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan [Social Media].

5. Malam Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa Gwamna Ganduje kan [Social Media] wanda ya samu wakilcin Malam Basiru Yusuf Shuwaki, Shugaban APC Social Media na Jahar Kano.

6. Ali Nuhu Muhammad, fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai cikin harshen Hausa [Kannywood].

7. Sadiya Kabala wacce ita ma babbar jaruma ce kuma fitacciya a masana’antar shirya Kannywood

8. Maryam Yahaya wacce ita ma fitacciyar jaruma ce mai tashe.

9. Adam A. Adam wanda shi ma fitaccen jarumi ne.

10. Sallau Na Dadin Kowa wanda shi ma shahararren jarumi ne kuma babban tauraro cikin shirin dadin kowa.

Cikin jawabin da ya gabatar, Malam Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamna Ganduje kan [Social Media], ya yaba tare da godewa [BNMC] reshen jihar Kano, kan dumbin gudunmawar da kungiyar ta bayar har aka kai ga samun nasara. Ya kuma ba wa kungiyar tabbacin cigaba da yin aiki tare domin shaidawa duniya ayyukan alkairan Ganduje a jihar Kano.

Shi ma a nasa jawabin, mai girma Sardaunan Kano, Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi godiya tare da yabawa aikace-aikacen wannan cibiya, ya kuma ja hankalin Matasa da su cigaba da gwagwarmaya da sannu za su kai ga nasarar cimma muradansu.

Shi ma a nasa jawabin, Malam Bashir Ahmad, mai taimakawa Shugaba Buhari kan [Social Media], ya bayyana farin cikinsa da wannan taro, inda ya bayyana nasarar da aka samu a matsayin nasara daga Allah, gami da godiya ga al’ummar da su ka samu damar halartar wannan taro.

Sauran wadanda su ka yi jawabi sun hada da: Rukayya Umar Farouk, wacce ta gabatar da jawabin maraba, sai Samira A. Usman wacce ta gabatar da takardar kan nasarorin da Matasa su ka samu a Nageria, domin zaburarwa ga sauran Matasa masu tasowa.

Dumbin al’umma ne su ka samu damar halartar taron, ciki har da mutanen Jihohin: Kaduna, Katsina, Yobe, Borno, Jigawa. Da sauran mahalarta ciki da wajen Kano. Duk domin nuna farin cikinsu kan nasarar lashe zabe da mai girma gwamna Ganduje ya yi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like