An gudanar da bikin ranar tunawa da yan mazan jiya


Shugaban kasa Muhammad ya sanya furanni tare da karbar faretin ban girma a wurin bikin tunawa da sojojin da suka mutu.

Ana gudanar da wannan bikin ne na tunawa da jami’an sojan a kowace ranar 15 ga watan Janairu na kowace shekara.

Sai dai bikin na ranar Juma’a ya tafi ya bar abin fada bayan da tattabarun da shugaban kasa ya saka daga cikin keji suka ki tashi.

A kowace shekara akan saka fararen tattabaru a cikin keji inda shugaban kasa yake bude su su tashi fur sama a matsayin wata alama ta zaman lafiya. Amma a wannan karon tattabarun sun gaza ta shi zuwa ko’ina.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 105

You may also like