A gobe Juma’a ake sa ran daura auren dan shugaban kasa Yusuf Muhammadu Buhari da amaryarsa Zahra Nasiru Ado Bayero, a karamar hukumar Bichi dake jihar Kano.

Tun daga jiya Laraba aka baza jami’an tsaro a ciki da wajen jihar musamman a garin bichi inda za’a gudanar da daurin auren bayan sallar Juma’a.

Shugaba Muhammadu Buhari da wasu hamshakan mutane daga ciki da wajen Najeriya za su halarci bikin, bayan nan kuma a ranar Assabar gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai yi bikin nadin sirikin ns shugaban kasar wanda shi ne sarkin Bichi

A cewar shugaban kwamitin shirye shirye na bikin Shehu Ahmed za’a kafa tarihi a ranakun Juma’a da Asabar a karamar hukumar Bichi inda za’a daura auren dan shugaban kasa da yar’sarkin garin da kuma nadin sarautar.

Ango Yusuf dai ya kasance da namiji tilo ga shugaba Muhammadu Buhari da uwargidansa Aisha Buhari.