An Gano Wasu Masu Cushe Cikin Albashin Ma’aikatan Jihar Bauchi


A jiya ne Jami’an tsaro suka fitar da rahoto kan wasu mutane da aka cafke masu zambatar jihar Bauchi milyoyin kudade a duk karshen wata da sunan biyan fansho. Inda wadanda ake zargin suka amza laifinsu ba tare da wahalar da huukuma ba.

Hukumomi sun bayyana sunayen su da kuma hotunan su ga manema labarai domin ya zamo darasi ga ‘yan baya.

(1) Yasir Sulaiman mai shekaru 37 mazaunin unguwar Bayan Airport ya cusa sunayen mutane biyu, hakan ya sa yake karbar N320,000 duk karshen wata har na tsawon watanni 23, jimillar kudin da ya zambaci jihar Bauchi ya kama naira milyan 7.360,000

(2) Umar Mohammed Madara dan shekara 49, mazaunin Ibrahim Bako quarters ya cusa sunan mutum daya, wanda yake karbar N120,000 duk wata har tsawon watanni 6 wanda jimillar kudin da ya zambaci jihar Bauchi ya kai naira 720,000.

(3)Samaila Musa mai shekaru 38 mazaunin unguwar Federal Low-cost ya cusa sunayen mutane biyu, hakan ya sa yake karban N65,000 da N85,000 duk karshen wata har tsawon watanni 18. Jimillar kudin da ya zambaci jihar Bauchi sun kai kimanin naira milyan 2, 700,000.

(4)Garba Bala mai shekaru 39 mazaunin unguwar Tirwun ya cusa sunan mutane biyu, yana karban N300,000 duk karshen wata har na tsawon watanni 36 wanda jimillar kudin daya zambaci jihar Bauchi ya kai naira milyan 10.800,000.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like