An gano wacce ta kashe jami’in difilomasiyar Najeriya a kasar Sudan


A cewar ma’aikatar wajen Najeriya wata yar kasar Sudan wacce asalinta yar Najeriya ce ita ce ta kashe Habibu Almu wani jami’in difilomasiya da aka kashe a Khartoum babban birnin Kasar Sudan.

Tope Elia-Fatile mai magana da yawun ma’aikatar, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce matar da ake zargi ta kashe almu a gidansa dake rukunin gidajen ma’aikata a ranar Alhamis.

Bayan kamawa da kuma binkice jami’an tsaron kasar ta Sudan sun kama,Ina Khalid Maikano da zargin cakawa Almu wuka.

“Yayin da hukumomi suke bincike sun gano cewa wacce ake zargin ta sace wasu daga cikin kayan marigayin ciki har da kudi.”

Mai magana da yawun ma’aikatar ya cigaba da cewa tuni wacce ake zargin ta amince da aikata laifin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like