An gano inda aka binne gawar wanibyaro da aka yi garkuwa da shi


Rundunar ‘yan sandar jihar Kano karkashin jagorancin Operation Puff-Adder No Any Criminal Count Out, sun gano inda barayin mutane suka binne yaron nan mai shekaru 5 da haihuwa bayan da suka sato shi daga Unguwar Darmanawa dake nan Kano.

Kuma an kama wani matashi kanin mahaifiyar yaron da aka sata wanda ake zargin sa da saka hannu kuma har ya amsa laifin sa, Ya kuma bayyana yadda abun ya faru a baya dai sun nemi iyayan yaron dasu bayar da Naira miliyan 50 ana ciniki su ka dawo miliyan 20 daga karshe da yaron ya mutu suka bukaci a basu dubu dari, ya shiga hannu ne bayan jami’an tsaro sun bibiyi lambar wayar da suke amfani da ita sai ya shaida musu yadda abun ya faru inda ya ce Allura suka yiwa yaron a karshe ya mutu.

Sai dai ya ce ba shi kadai ne mai laifin ba yana da mataimaka mutum biyu, kuma nan take ya kai jami’an tsaro wurin da suka binne yaron a Sheka sabuwar Abuja dake jihar Kano tare da damke sauran mutum biyun da ya lissafawa jami’an ‘yan sanda yanzu suna hannu domin yin kwakwaran bincike akai daga karshe su girbi abun da suka shuka.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like