An gano gawarwakin mutane 30 cikin kabari daya a Benue


Akalla gawarwakin mutane 30 aka gano cikin wani babban kabari a kauyen Gbatse dake karamar hukumar Ushongo ta jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa an gano kabarin ne a harabar gidan wani da ake zargin jagoran masu garkuwa da mutane ne da ya dade yana addabar matafiya dake bin hanyar yankin.

Hakan ya kawo rudani a yankin inda mutane suka rika tururuwa zuwa wurin da abin ya faru ya yin da aka yi zargin cewa wasu daga cikin mutanen sun gano yan uwansu cikin mamatan.

Gano wurin ya biyo bayan kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da yan sanda suka yi inda ya amsa laifin kisan wani mutum kuma ya yi musu jagora zuwa wajen.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Catherine Anene ta tabbatar da faruwar.


Like it? Share with your friends!

1

You may also like