An gano gawar dan kasar Lebanon da aka yi garkuwa da shi a Kano


Jami’an ƴansanda a jihar Kano sun samu nasarar gano gawar wani Injiniyan gine-gine dan kasar Lebanon wanda aka yi garkuwa da shi ranar Talata.

Wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba sune suka yi garkuwa da marigayin da safiyar ranar Talata lokacin da yake duba aikin titin kasa da ake yi a shatale-talen Dangi a cikin birnin Kano.

Ya yin da aka kashe direbansa nan take a wurin shi kuwa anyi awon gaba da shi ya zuwa wani da ba a sani ba.

Marigayin na aiki ne da kamfanin gine-gine na Triacta.

Da yake tabbatar da mutuwarsa mai magana da yawun rundunar yansandan jihar, Abdullahi Haruna ya ce an gano gawar Injiniyan ne akan hanyar Kano zuwa Maiduguri da yammacin ranar Alhamis.

Abdullahi ya kara da cewa ba a kama kowa ba game da lamarin amma rundunar na cigaba da gudanar da bincike.

Comments 3

Your email address will not be published.

You may also like