An Gabatar Da Mutane 19 Da Suka Kashe Janar Alkali


Rundinar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Filato ta gabatar da ‘yan kabilar Berom wadanda ake zargi da hallaka Janar Idris Alkai ga manema labarai a birnin Jos.

Ga sunayensu kamar haka;

1. Pam Chuwang Kim ‘dan shekara (32) yana da cikakken masaniya game da wadanda suka kashe janar Idris Alkali.

2. Pam Chuwang Dung ‘dan shekara (19) yana da masaniya game da kisan Janar Idris Alkali.

3. Michael James ‘dan shekara 22 yana da zama a kauyen Doi ya kalli lokacin da ake kokarin hallaka Janar Idris Alkali, kuma yasan dukkan mutanen da suka hallakar Janar din amma ya boye har sai bayan da aka kamashi kafin ya bayyana.

4. Dung Pam ‘dan shekara 26 matashi ne daga kauyen Doi an kamashi da bindiga tare da harsashin bindiga.

5. John Alkali ‘dan shekara 21shima an kamashi da bindiga da harsashin bindiga.

6. Rebecca Gyang Pam mace ce ‘yar shekara 35 tana da zama a kauyen Doi taba daya daga cikin matan da suka jagoranci zanga-zangar hana sojoji aikin yashe kududdufin Dura-Du wanda daga karshe aka gano motar marigayi Janar Idris Alkali a ciki, ta jagoranci zanga-zangar ne domin boye laifin suka aikata.

7. Yohanna Dung ‘dan shekara 61 yana sana’ar kafinta, sojoji ne suka kamashi lokacin da suke bincike.

8. Stanley Onuchukwu ‘dan shekara 34 yana da masana’antar kera bulok kusa da kududdufin da aka samu motar Janar Idris Alkali a ciki, yana da cikakken masaniya akan lokacin da aka tura motar Janar Idris cikin wannan kududdufin amma ya boye bayanan har sai bayan da aka kamashi ya bayyana.

9. Nenfa jwanan ‘dan shekara 22 yana aikin kera bulok a karkashin masana’antar Stanley Onuchukwu ya kalli lokacin da ake tura motar Janar Idris Alkali cikin kududdufi amma ya boye labarin har sai bayan da aka kamashi.

10. Michael Peter yana aiki a karkashin masana’antar buga bulok na Stanley Onuchukwu yana da bayanai game da yadda aka jefa motar Janar Idris Alkali cikin kududdufi, kuma ya ga lokacin da aka tare hanyar da janar idris Alkali yazo wucewa a ranar 3-9-2018 amma ya boye bayanan har sai bayan da aka kamashi.

11. Maxwell Dadel yana da bayanai game da yadda aka jefa motar Janar Idris Alkali a cikin kududdufi amma ya boye har sai bayan da aka kamashi.

12. Simon Sule ‘dan shekara 27 sojoji ne suka kamashi lokacin suke bincike yana da zama a kauyen Dura-Du.

13. Paul Bot Gyangzee ‘dan shekara 52 yana da gidan sayar da abinci da mashaya an kamashi lokacin da sojoji suke bincike, bincike ya bayyana cewa manyan wadanda ake zargi akan kisan Janar Idris Alkali a wajenshi suka hadu suku tsara ta’addancin, kuma ya san su.

Ga bayanin wadanda rundinar ‘yan sanda ta bayyana nemansu ruwa a jallo da irin laifukan da suka aikata.

14. Stephen Chuwang ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka tone gawar Janar Idris Alkali a ranar 29-9-2018 daga kauyen Doi-Du suka kai gawar kauyen Gushwet Shen suka jefa a rijiya, kuma bayan an kamashi shine ya jagoranci jami’an tsaro zuwa inda aka samo gawar Janar din daga rijiya.

15. Timothy Chuwang shine wanda ya tuka motar Janar Idris Alkali daga Doi-Du zuwa kududdufin Dura-Du ya tora motar zuwa cikin kududdufi tare da taimakon wasu a ranar 03/09/2018.

16. Mathew Chuwang Rwang shine shugaban matasan garin Doi-Du
an ambaci sunansa daga cikin wadanda suka tone gawar Janar Idris Alkali daga Doi-Duas suka kai gawar kauyen Gushwet-Shen.

17. Yakubu Rapp shine sarkin Dura-Du wanda a garinsa ne aka samu motar Janar Idris Alkali yana da masaniya akan dukkan abinda ya faru saboda matasan kauyen suna matukar girmamashi.

18. Pam Gyang Duns ‘dan kauyen Doi-Du kuna shine mai unguwar Latiya, shine babban abokin Da Chuwang yafi shahara da Mourinho wanda shine babban wanda ake zargi kuma har zuwa yanzu ba’a kamashi ba ya gudu, yana daga cikin wadanda suka hadu suka hallaka Janar Idris Alkali.

19. Moses Gyang ‘da ne ga Pam Gyang Dung wanda yafi shahara da Boss daya daga cikin wadanda suka hallaka janar Idris Alkali kuma har yanzu ba’a kamashi ba ya gudu, an samu bindiga a gidanshi lokacin da ake bincike.

Rundinar ‘yan sanda tace mutane biyun da suka gudu ana kokarin kamosu domin su fuskanci hukunci, wadannan kuma da suke hannu za’a gurfanar dasu a gaban kotu.

Muna mika sakon godiya da jinjina ga jami’an tsaro musamman wanda ya jagoranci binciken gano karshen makomar Janar Idris Alkali Birgediya Janar Umar Muhammad, jinjina ga rundinar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, hakika sun nuna kwarewa da bajinta, sunyi aiki ba dare ba rana har sai da aka gano karshen makomar Janar da wadanda suka hallakashi, muna godiya kwarai dagaske Allah Ya saka muku da alheri Ya kara muku girma da daukaka a cikin aikinku.

Allah Ka sa wadannan azzalumai maguzawa ‘yan ta’adda su fuskanci mummunan hukunci su wulakanta tun daga nan duniya fiye da yadda suka wulakanta gawar Janar Idris Alkali.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like