An Fara Gasar Manufofin Gwamnatin Atiku Abubakar


A jiya lahadi ne aka bude gasar manufofin dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar inda aka baiwa duk dan Nijeriya damar shiga gasar ta yadda zai iya kalubalanci manufofin dan takarar.

Gasar mai taken, ” #LetsGetNigeriaWorkingAgain” wato, ” yadda za Mu sake farfado da Nijeriya” an tsara shi ne, yadda za a tantance mutane shida wadanda za a ba su damar minti daya kacal a gidan talbijin na kasa inda za a nuna bidiyon da suka shirya kan ra’ayinsu game da farfado da Nijeriya.

Duk wanda ke sha’awar shiga gasar, zai dauki hoton Bidiyo na kansa na minti daya kacal inda zai bayyana yadda za a ciyar da Nijeriya gaba sannan ya wallafa bidiyon a shafinsa na ” Facebook” tare da makala taken: #LetsGetNigeriaWorkingAgain-# da kuma asalin jiharsa.


Like it? Share with your friends!

-2
77 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like