An Fadi Sakamakon Lissafin Buhun Gero Da Akayi A Kwana 105 Ana Lissafawa


Makirga gero sun fadi sakamakon lisafin buhun gero wanda suka share kimanin kwana dari da biyar (105) suna lisafin buhun na gero .Anfadi sakamakon lisafin buhun na gero ne a fadar mai martaba Sarkin Yauri dake jihar kebbi da misalin karfe 10:30am

A yayin gudanar bikin an dai samu halartan manyan mutane Hadi da manema labarai daban daban da Kuma wakilai na wadanda Basu samu Daman Zuwa ba,inda mai magana da yawun masu kirga buhun gero Wato Ahmed Sarkin Yaki Yauri ya sanar da sakamakon lisafin kamar haka:- 11,979 868 wato milliyan Sha daya, da dubu Dari Tara da saba’in da tara da Dari takwas da sittin da takwas

Daga karshe dai an Karrama Matasannan da suka kirga Buhun GERO kaf, bayan wata gardama data kaure tsakanin su.

Inda aka tabbatar da 11,979,868 shine adadin kwayar GERO da ke cikin Buhu guda.

Yanzu dai ta tabbata da cewa ‘yan Najeriya sunfi Buhun GERO yawa.

Masu karatu kome zaku ce Akan Wannan Batu?


Like it? Share with your friends!

2
96 shares, 2 points

Comments 5

Your email address will not be published.

  1. BAJINTA,RAWAR GANI!!!
    Abun mamaki,da an ce min yawan kwayoyin gero zai tsaya iya haka ba tare da an lissafa ba,ba zan yarda ba.Kuma wannan bajinta ce ta musamman da ta cancanci jinjinawa,domin kuwa ina ganin ita ce ta farko a wannan yanayi.A gaishe su.

You may also like