An dauke Melaye daga Ofishin DSS ya zuwa na SARS


Jami’an ƴansanda sun dauke Dino Melaye sanata mai wakiltar mazabar yammacin jihar Kogi a majalisar dattawa, daga ofishin hukumar tsaro ta DSS ya zuwa ofishin rundunar ƴansanda mai yaki da yan fashi da makami wato SARS dake Guzape a Abuja.

A ranar Juma’a ne jami’an ƴansanda suka dauke sanatan daga asibitin rundunar ƴansanda dake Abuja ya zuwa asibitin hukumar tsaro ta DSS bayan da ya koka kan cewa baya samun kulawa.

A asibitin ƴansanda an tabbatar da cewa Melaye na cikin koshin lafiya kuma zai iya fuskantar shari’a.

Wani makusancin sanatan ya fadawa jaridar The Cable ranar Asabar cewa basu san mataki na gaba ba da ƴansandan za su dauka.

“Sun dauke shi ya zuwa ofishin SARS dake Guzape, ƴansandan sun dauke shi batare da sunce komai ba,” a cewar makusancin nasa.


Like it? Share with your friends!

1
70 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like