An dage zaman majalisun kasa bisa rasuwar Funke Adedoyin


Sanatoci da kuma yan majalisar wakilai ta tarayya sun dage zamansu na yau bisa rasuwar Funke Adedoyin wata yar majalisar wakilai.

Ya yin da mambobin majalisar wakilai za su dawo aiki ranar Alhamis su kuwa yan majalisar dattawa za su cigaba da aiki daga gobe Laraba.

Adedoyin ta mutu ranar 27 ga watan Satumba tana da shekaru 56 bayan fama da cutar sankara.

Har ya zuwa lokacin mutuwarta yar majalisar na wakiltar mazabar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-ero dake jihar Kwara.

Yar majalisar ta taba riƙe muƙamin ministar matasa da cigaban jama’a da kuma muƙamin karamar ministar lafiya.

Bisa al’ada majalisun sukan tafi hutu idan mamba a daya daga cikin majalisun ya mutu.


Like it? Share with your friends!

-1
74 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like