An ceto mutane biyar daga baraguzan ginin bene da ya ruguzo a Legas


Mutane biyar aka ceto yayin da wani ginin bene mai hawa biyu ya rikito a yankin Ojuelegba dake jahar Legas.

Ginin dake kan layin Rufa’i ya rikito da tsakar daren ranar Juma’a.

Gwamnatin jihar ita ta sanar da faruwar lamarin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Mutane biyar aka ceto daga wani ginin bene mai hawa biyu da ya ruguzo da asubahin yau ranar Juma’a, 25 ga watan Oktoba 2019 dake layin Rufa’i idan kabar layin Makinde a Ojuelegba,” sakon ya ce.

Sanarwar ta cigaba da cewa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, ta tura jami’anta ya zuwa wajen domin ceto mutanen da abin ya rutsa da su.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like