An Bukaci Buhari Ya Saki Zakzaky A Birnin Landan


Da yammacin yau, bayan abubuwan da suka faru tsakanin mabiya Sheikh Zakzaky da Jami’an tsaron Nijeriya wanda ya jawo asarar rayuka na mabiyan Shekih Zakzaky, al’ummar musulmi dake kasar Landan sun yi zanga-zanga kan neman a saki Malamin domin lafiyarsa.

Sun gudanar da zanga-zagar ne a ofishin jakadancin Nijeriya dake kasar Ingila, inda suka daga manyan hotunan Sheikh Zakzaky suna karanta abubuwan dake faruwa.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da suka yi fita irin wannan.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like