Su ma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi Allah wadai da matakin, wanda ya biyo bayan kokarin da gwamnatin kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka ta yi a lokutan daidaita tsarin kafofin sada zumunta.

Masu kamfanonin sadarwar Najeriya sun bi umarnin gwamnati ranar Juma’a na dakatar da shiga shafin na Twitter har abada.

Ofisoshin diflomasiyya na Tarayyar Turai, Amurka, Biritaniya, Canada da Ireland sun ba da wata sanarwa ta hadin gwiwa da yammacin Asabar inda suka yi Allah Wadai da haramcin.

“Haramtawa tsarin bayyana ra’ayi ba shi ne mafita ba,” in ji su.

Najeriya kuwa ta yi kashedi da cewa za ta hukunta duk masu karya dokar.

“Babban Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ba da umarnin a gurfanar da wadanda suka karya dokar Tarayyar a kan ayyukan Twitter a Najeriya cikin gaggawa.” In ji mai magana da yawun Babban Atoni Janar na Tarayyar, Umar Jibrilu Gwandu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “Amnesty International” ta yi Allah wadai da wannan haramci, tare da yin kira ga Najeriya “da ta gaggauta janye dakatarwar da aka yi ba bisa ka’ida ba.”