Amosun ya yi ganawar sirri da Buhari


Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya yi ganawar sirri da shugaban kasa, Muhammad Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Amosun ya isa fadar shugaban kasar da misalin karfe 02:50 na rana inda ya wuce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa.

Gwamnan na Ogun na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyar APC dake neman a cire shugaban jam’iyar Adam Oshimhole kan zaben fidda gwani yan takarkaru daban-daban na jam’iyar da aka gudanar.

A farkon wannan makonnan Oshimhole ya amsa tambayoyi daga jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS bisa zargin da ake masa na aikata cin hanci da rashawa.

Uwar Jam’iyar APC ta ki yarda da dantakarar da gwamnan yake so ya gaje shi, Abdulkabir Adekunle Akinlade inda ta maye gurbinsa da sunan Dapo Abiodun.


Like it? Share with your friends!

-1
58 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like