Yayin baiyana matakin, sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce kasar ta damu matuka kan yadda rikicin ke kara ta’azzara tare da yin kira ga bangarorin biyu da su hau teburin sulhu.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Kamaru dai sun zargi bangarorin biyu da gasa wa junansu aya a hannu, zargin da gwamnatin ta musanta ta na mai cewa, a lokuta da dama ta kama jami’an soji da laifin kisa ko cin zarafi.

Yankuna biyu na masu magana da Turancin Ingilishi dai na Kamaru ya sha fama da rikici tun a shekarar 2017, lamarin da ya haifar da asarar rayukan mutane fiye da dubu 3 yayin da wasu kimanin dubu dari 7 suka rasa matsugunnansu.