A karon farko bayan shekaru 19 hukumomin Amirka sun sako wani ba Amirke dan asalin Moroko da aka tsare a Guantanamo ba tare da tuhuma ba kan zargin ta’addanci.

Yanzu haka dai kusan mutane 800 ne suka dandana zaman kurkukun Guatanamo Bay. Akwai mutane 39 da ke tsare hayar yanzu 10 daga ciki sun cancanji sauya musu sheka, zuwa asalin kasashensu kamar Yemen da Pakistan da Tunisiya da Aljeriya da kuma hadaddiyar daular Larabawa Dubai.