Kotun kolin Amirka ta sake tabbatar da dokar nan ta haramta wa bakin haure masu neman mafaka da su ka shiga kasar ta barauniyar hanya, damar mallakar takardun zama yan kasar na dundundun.

Dokar na daya daga cikin dokokin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya assasa, wadda kuma sabuwar gwamnatin shugaba Joe Biden ke kokarin sauyawa.

Hukuncin na kotun dai zai cigaba da shafar dubunnan yan gudun hijira da ke zaune a kasar ta Amirka domin nemar mafaka.