Ambaliya ta mamaye wata makarantar firamare


Ambaliyar ruwa ta mamaye baki dayan harabar makarantar firamare ta Ezigbo dake kauyen Okukwa, Amasea a karamar hukumar Awka North dake jihar Anambra.

Hakan ya jawo dalibai sama da 650 da kuma malamansu kasa isa cikin ajujuwansu.

A kokarin maganin matsalar, yan kwanakin baya hukumar makarantar ta tara kasa da duwatsu domin samar da hanya amma yan kalilan ne suka samu damar shiga ajujuwan na su saboda tsoron ambaliyar.

Da take magana kan ambaliyar shugabar makarantar, Mrs. Letecia Umeadi ta yi kira ga ma’aikatar muhalli da kuma sauran hukumomin da abun ya shafa da su kawo musu dauki domin su samu damar isa ajujuwansu.

A cewarta ambaliyar ta mamaye illahirin makarantar kuma babu yadda za su yi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like