Ambaliya ta lalata gonaki 3000 da gidaje 120 a Jigawa


Amabaliya sakamako mamakon ruwan sama ta lalata gonaki sama da 3000 da gidaje 120 a kauyen Zugo dake karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

A Cewar kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, jami’in yada labarai na yankin, Alhaji Sanusi Doro ya fadawa manema labarai ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ranar Talata da tsakar dare.

Ya ce ambaliyar ta lalata hanya a yankin abin da ya kawo tarnaki ga zirga-zirgar mutane da safarar amfanin Gona.

Ya yi kira ga hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma gwamnatin jihar da suka kawowa mutanen da abin ya shafa da abinci da kuma magunguna.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like