Amarya Ta Kashe Angonta Da Guba A Jihar Kano


Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta cafke wata amarya, Sadiya Umar wacce ake tuhuma da kashe angonta Sani Umar makonni biyu bayan daura aurensu.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, Magaji Musa Majiya ya shaidawa manema labarai cewa ana zargin Sadiya da sanyawa angonta Sani Umar guba ne a abincinsa ranar Alhamis 4 ga Janairu, 2018 a gidansa dake unguwar Yakasai.

Magaji Musa Majiya ya ce marigayi Sani Umar ya rasu ne a asibitin Koyarwa na Aminu Kano kwana guda bayan cin abincin mai dafi.

Kakakin ‘yan sandan ya ce ‘yan uwan angon ne suka shigar da karar amaryar a ofishin ‘yan sanda dake unguwar Kofar Wambai a birnin Kano.

Sai dai ya ce da fari amaryar da ake zargi ta tsere daga gidan mijinta sai a ranar Litinin aka yi nasarar damke ta.
Sadiya Amarya ta dade tana tambayar kawayen ta, wai shin matan da suke kashe mazajensu, dame suke amfani. A ranar da zata kashe mijin nata ne ta aiki wani yaro yaje ya siyo mata shinkafar Ɓera inda da itane ta dafawa mijin nata taliya sannan ta kuma takura masa sai da yayi loma uku kafin ya fita. 

A baya bayan nan dai ana yawan samun labaran mata dake hallaka mazajensu a sassa dabam-daban na Nigeria, abinda masana ke dangantawa da saurin fushi da kuma gajen hakuri.


Like it? Share with your friends!

-2
118 shares, -2 points

Comments 6

Your email address will not be published.

  1. Maza, dole ne abinda yafi wannan yafaru,domin ManZon Allah s.A.w yafada muku,siffar Macen dayaka Mata ku aure.

  2. Duka laifin iyayene dasuke tilastawa yayansu auren dole dakuma zaman sure Wanda chikinsa babu dadi ankasa daidaitawa.nabiyu iyaye bass maida hankali a karatun addini dakuma fadakarwa.kashe maza yayi yawa yanzu kuma sai andage da hadakai da kafafan TV da radio domin asamu arage wannan Abu.

You may also like