A hirar shi da Muryar Amurka, daya daga cikin al’umar yankin, Malam Yusuf Ibrahim Udawa ya ce baya ga hare-haren yan-bindiga, su kan kuma shiga su karbi kudaden al’uma sannan su yi lalata da matan mutane.

Wannan korafi dai na zuwa ne kwanaki biyu da fitar da rahoton tsaro da gwamnatin jahar Kaduna ta yi inda ta bayyana nasarorin da ta ke samu kan maharan dajin baki daya.

Kaduna dai na cikin jihohin Arewan maso yammacin da ke fama da hare-haren ‘yan-bindiga masamman dai satar dalibai wadda har yanzu akwai daliban makarantun da ba a dawo da su ba.

Saurare cikakken rahoton a sauti: