Allah Ya Yiwa Dan Masanin Tsafe Kuma Tsohon Dan Jarida Alhaji Sani Abdullahi Tsafe Rasuwa


INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJI’UN!

Allah ya yi wa Dan Masanin Tsafe kuma fitaccen dan jarida wanda ya taba zama wakilin rediyon Muryar Amurka, Alhaji Sani Abdullahi Tsafe, rasuwa.

Marigayi Sani Abdullahi Tsafe ya rasu ne yau a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja, bayan wata jinya da ya yi fama da ita.

Za a sanar da lokacin da za a yi masa jana’iza nan gaba kadan.

Kafin rasuwar Alhaji Sani Abdullahi Tsafe shi ne babban mai bai wa Gwamnan jihar Zamfara shawara kan al’amura na musamman.

Muna taya al’ummar jihar Zamfara, Gwamnati da iyalansa da daukacin masoya ta’aziyyar wannan babban rashi da aka yi. Allah ya gafarta masa ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa da mu baki daya.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like