Alkalin Alkalai Bai Halarci Zama Ba A Lokacin Da Kotun Koli Ta Fara Yanke Hukuncinta Kan Zaben Gwamnan Jihar Kano


Rahotanni sun nuna cewa Shugaban alkalan Nijeriya, Jastis Tanko Muhammed bai halarci zama ba a lokacin da kotun koli ta fara yanke hukuncinta kan karar da aka daukaka kan zaben gwamnan jihar Kano.

A madadinsa, Jastis Sylvester Ngwuta ne ke jagorantar kwamitin alkalan mai dauke da membobi biyar.

Sauran Alkalan sun hada dan Jastis Kudirat Kekekere-Ekun, Jastis Olukayode Ariwoola, Jastis Amina Augie da kuma Jastis Uwani Abba-Aji.

Tuni dai Kotun Kolin ta yi watsi da karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar, inda ta tabbatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin zababben gwamnan jihar Kano a zaben Maris, 2019.

Alkalan kotun gaba daya karkashin jagorancin Jastis Sylvester Ngwuta sun yi ittifakin cewa karar da Abba Kabir Yusuf ya shigar bata da karfi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like