Alhazan Zamfara sun sake samun ragin kudin aikin hajji


Hukumar Alhazai ta kasa ta ce alhazan da suka fito daga jihar Zamfara sun samu karin ragin riyal 200 kan kudin kujerar da suka biya.

Shugabar sashen hulda da jama’a a hukumar alhazan, Fatima Sanda Usara ita ta bayyana haka cikin wata sanarwa inda ta ce an samu ragin ne bayan sake tattaunawa da mamallakin gidan da alhazan jihar suka sauka a birnin Makka.

Adadin kudin ya kama ₦16492.48 a kudin Najeriya hakan yasa kudin kujera aikin hajji daga jihar Zamfara ya koma ₦1, 467, 896.57.

Hukumar alhazan ta godewa gwamnan jihar,Bello Matawalle kan tattaunawar da aka yi da ta jawo ragin kudin.

Har ila yau hukumar ta yabawa hukumar alhazan jihar kan yadda ta tattaro kan alhazai duk da matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar.


Like it? Share with your friends!

-1
70 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like