AL’AJABI: An Gano Gashi, Auduga, Reza Da Gawayi A Cikin Wata Mata A Jihar Gombe


A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani abun al’ajabi ya faru da wata mata wadda ta bukaci a boye sunan ta a unguwar Fantami dake jihar Gombe. Inda ta yi ta fama da ciwon ciki na tsawon wasu kwaniki ana ta magani amma a banza. Sai ‘yan uwanta suka yanke shawarar kai ta wajen magani na gargajiya dake unguwar Bagadaza. Dawowarsu ke da wuya sai ta fara jin ba haya, shigar ta bayan gida ke da wuya kuwa sai ga wata kwalba ta fito ta al’urarta.

Bayan fitowar kwalbar sai ‘yan uwanta suka yanke shawarin bude kwalbar saboda ganin abunda ke ciki, budewar ke da wuya sai ga wasu abubuwa kamar haka gashi, gawayi, tsinkaye, auduga, farce da karyayyun reza.

Bayan an ga wadannan abubuwa sai wasu daga ciki suka ce a sa masa wuta sa wutar keda wuya kuwa ta fara ci har tafi karfin abun ba tare da kwalbar ta fashe ba, amma daga bisani ‘yan uwanta suke zargin sihiri aka mata. Kamar yadda Hassana Abdullahi SG ta bayyana wa majiyarmu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like