Akwai Yiyuwar Kashe Naira Biliyan 900 Kan Tallafin Mai
Wannan batu na zuwa ne bayan fara nazari kan kokarin gwamnatin Najeriya da shugaba Buhari ke jagoranta kan shirin fara aikin yin kasafin kudin shekarar 2022 da aka kiyasta cewa zai kai kimanin naira tiriliyan 13 da biliyan 910.

Minstar kudi Zainab Ahmad ta ce jumlar ainihin kasafin kudin shekarar 2022 shine naira tiriliyan 11 da biliyan 90, saidai idan aka hada da sauran hanyoyin shigowar kudade na gwamnatin Najeriya zai koma naira tiriliyan 13 da biliyan 91 sabanin naira tiriliyan 13 da biliyan 580 na bana.

Haka kasafin zai ci gaba da karuwa kamar yadda hasashen ministar kudi ya bayyana, inda ta ce a shekarar 2023, kasafin kudin Najeriya zai koma naira tiriliyan 15 da biliyan 450, kuma a shekarar 2024 za’a sami kari da zai kai kasafin kasar naira tiriliyan 16 da biliyan 770.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da Zainab Shamsuna Ahmad da ke zama ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, ta gabatar a yayin taro kan tsare-tsaren kashe kudi a matsakaicin zango na shekarar 2022 zuwa shekarar 2024 wanda aka fi sani da MTEF/FSP a ranar Alhamis.

Hajiya Shamsuna Ahmad ta kuma bayyana cewa za a sami gibin kaso 3.05 cikin 100 a kan kasafin shekarar 2022 da mu ke ciki duba da yanayin tattalin arziki da kasar ke ciki inda ta ce duk da gibin da za’a samu hakan na nufin ci gaba ne idan aka duba yadda aka sami gibin kaso 3.91 a kasafin shekarar 2021.

A cewar minista Shamsuna, gwamnatin tarayya za ta samar da kudaden kasafin kudin ne ta hanyoyin da suka hada da cefanar da wasu kadarorin gwamnati da kuma ciyo bashi daga ciki da wajen kasar domin cike gibin naira tiriliyan 5 da biliyan 62 a shekarar 2022.

Hajiya Shamsuna ta jaddada mahimancin cire tallafin mai sakamakon yadda wasu tsirarun mutane ke amfana da tallafin man fetur idan gwamnati ta ci gaba da biya tallafin saboda motocin hawa a Najeriya na manyan mutane ne da kuma yadda dukkan kasashe makwabta ke cin moriyar wannan tallafin na Najeriya ba wai ‘yan kasar kawai ba.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta bayyana aniyar duba yiwuwar fito da wani tsari da zai rage wa wadanda cire tallafin zai shafa radadin cirewar, kamar fadada hanyoyin samun kudadden shiga da ba zai shafi yan kasar ba ta fuskar biyan harajin cikin gida kamar yadda mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.