Akan cin hancin ₦2000 dan sanda ya harbe direba akan hanyar Abuja-Kaduna


Ana zargin wasu yan sanda dake bakin aiki akan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kashe wani direban mota bayan da suka nemi ya basu na goro har ₦2000 a cewar wata majiya da ta gana da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN.

Direban da ba a san ko waye ba, dan sandan ya harbe shi ne da safiyar ayua akan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

Sama da sa’o’i hudu aka shafe zirga-zirgar ababen hawa ta tsaya cak akan titin bayan da masu motoci yan uwan direban suka yi bore inda suka rufe hanyar.

NAN ta jiwo daga bakin wani da abin ya faru akan idonsa na cewa daya daga cikin yan sandan dake aiki a titin shine ya harbe direban bayan da yaki ba shi na goro.

Shima wani shedan ya bayyana cewa motar da direban yake ciki kirar J5 ce kuma yana dauke ne da shinkafa.


Like it? Share with your friends!

-1
92 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like