Aisha Buhari ta tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Kebbi


Mai dakin shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙauyuka daban-daban na jihar Kebbi.

Aisha Buhari ta bayar da kayan tallafin ne ta karkashin shirinta na tallafawa mata da ake kira Future Assured da kuma gidauniyar Aisha Buhari.

Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Atiku Bagudu ce ta jagoranci rabon kayan tallafin.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like