Aisha Alhassan Ta Halacci Zaman Taron Majalisar Zartarwa Ta Kasa 


Aisha Alhassan ministar harkokin mata ta isa wurin taron majalisar zartarwa ta tarayya da misalin karfe 10:45 na safe  inda ta samu kyakkyawar tarba daga sauran ministoci.

Taron wanda shugaban kasa Muhammad Buhari ya jagoranta an fara shi da karfe 11:00 na safe.

Tun bayan da wani fefan bidiyo ya bayyana inda a ciki ministar ta nuna goyon bayanta ga takarar Atiku Abubakar a zaben shekarar 2019,mutane da dama suke zargin ministar da rashin biyayya ga shugaban kasa Muhammad Buhari.

Jam’iyar APC da kuma gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai sun yi kira ga shugaban kasa kan yadda koreta daga gwamnatinsa.

Kafin shiga wurin zaman majalisar sai da ministar ta gaisa da abokin aikinta Kayode Fayemi, ministan ma’adanai wanda ke tare da shugaban ma’aikata Abba kyari da kuma babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like