Aikin da nayi na shekara uku yafi na shekaru 16 a karkashin mulkin Jam’iyyar PDP – Buhari


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce gwamnatinsa ta cimma nasarori masu yawa cikin shekaru uku fiye da abinda da jam’iyar PDP ta cimma a shekaru 16 da ta shafe tan mulki .

Buhari ya bayyana haka ranar Litinin a fadar sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Sanusi dake Dutse babban birnin jihar Jigawa, a cewar mai taimakawa shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Ya ce faduwar darajar man fetur da ta fara a farkon shekarar 2016 bai hana gwamnatinsa daura damba na cimma wasu manufofin cigaba inda ta samu tarin nasara cikin shekaru uku fiye da shekaru 16 na jam’iyar PDP.

Shugaban yace gwamnatinsa na cika alkawarurrukan da ta dauka ta hanyar tsantsaini wajen kashe dukiyar jama’a domin kawo karshen barnatar da kudaden gwamnati.

Ya ce gwamnatinsa na samun goyon baya ne saboda yan Najeriya sun fahimci irin halin da ta gaji kasar.

Shugaban kasa Muhammad Buhari na yin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Jigawa inda zai kaddamar da wasu ayyuka.


Like it? Share with your friends!

2
178 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like