Ahmad Musa ya samu karuwar ɗa namiji


Danwasan kwallon kafar kungiyar Super Eagle, Ahmad Musa ya sanar da samun karuwar da namiji.

Danwasan mai shekaru 25 ya sanar da haihuwar matar tasa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Wannan ne jariri na farko da suka haifa da matarsa mai suna Juliet duk da cewa yana da ya’ya biyu da matarsa ta farko da suka rabu mai suna Jamila.

A yanzu haka dan wasan na kasar Austria tare da tawagar ƴanwasan ƙwallon kafa ta Leicester City.

Idan za a iya tunawa a ranar Litinin, William Troost-Ekong dan wasan ƙwallon ƙafa na kungiyar shima ya yi murna da samun karuwar da namiji.


Like it? Share with your friends!

-1
56 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like