An ayyana sanata Ahmad Lawan a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa.

Hakan ya biyo bayan zaben da aka gudanar tsakaninsa da Sanata Muhammad Ali Ndume daga jihar Borno.

Zaben ya gudana ba tare da wani tsaiko ba ya yin zaman kaddamar da majalisar dattawa ta tara.

Akawun majalisar Muhammad Sanni-Omolori shine ya jagoranci zaben inda a karshe bayan an kammala Lawal ya samu kuri’a 79 ya yin da Ndume ya samu kuri’a 28.

Zababbun sanatoci 107 ne suka kada kuri’a a zaben.