Afrika ta Kudu:yawan ‘yan Najeriya masu sha’awar dawowa gida ya kai 640


Abike Dabiri-Erewa shugabar hukumar dake lura da yan Najeriya mazauna kasashen waje ta ce yan Najeriya 640 ne suka nuna sha’awarsu ta dawowa gida daga kasar Afrika ta Kudu.

Dabiri Erewa ta bayyana haka ranar Litinin lokacin da take amsa tambayoyi daga yan jarida.

Tun da farko, Godwin Adama babban jami’in difilomasiya a ofishin jakadancin Najeriya dake Afrika ta Kudu ya bayyana cewa yan Najeriya 400 ne suka nuna sha’awarsu ta dawowa gida.

Adama wanda ya fadawa kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN haka ranar Lahadi ya ce karin yan Najeriya da dama na cigaba da nuna sha’awarsu ta dawowa.

Yan Najeriya da kuma sauran kasashe sun fuskanci hare-hare daga yan kasar dake adawa da kasancewar baki yan kasashen waje a kasarsu.

Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya yi tayin kwaso yan Najeriya kyauta daga kasar ta Afrika ta Kudu.

Lokacin da ta bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa kan yan Najeriya mazauna kasashen waje ranar Litinin,Dabiri Erewa ta ce jirage biyu ne za su kwaso yan Najeriya zuwa gida.

Ta ce gwamnatin tarayya na bukatar abiya diyya ga mutanen da abin ya shafa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like