Afrika ta Kudu:kason farko na yan Najeriya sun sauka a birnin Legas


Jirgin saman kamfanin Air Peace wanda ya dauko yan Najeriya daga kasar Afrika ta Kudu da suka baro kasar saboda harin da ake kai wa baki ya sauka a filin jirgin saman na Murtala Muhammad dake Lagos da misalin karfe 09:35 na daren ranar Laraba.

Abike Dabiri-Erewa shugabar hukumar dake lura da yan Najeriya mazauna kasashen waje ita ta jagoranci jami’an gwamnati da suka tarbe su.

Sauran wadanda suke wurin sun hada da jami’an hukumar lura da shige da fice ta Najeriya dana hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da sauransu.

Da yake magana da manema labarai daya daga cikin mutanen da suka dawo gida mai suna,Jude Anthony ya ce gwamnatin kasar Afrika itace kanwa uwargamin rikicin kin jinin baki dake cigaba da ruruwa a kasar.

Dabiri-Erewa ta ce jumullar yan Najeriya 187 ne aka kwaso daga kasar ta Afrika ta Kudu.


Like it? Share with your friends!

-2
84 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like