Afrika ta kudu: Gwamnatin tarayya za fara dawo da yan Najeriya gida a gobe Laraba


Gwamnatin tarayya ta ce ranar Laraba zata fara kwaso yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu bayan hare-haren da suka fuskanta na kin jini baki.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada umarnin kwaso dukkanin wadanda suka yi niyar dawowa gida.

Babban jami’in difilomasiya a ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ta Afrika ta Kudu, Godwin Adamu jiya a birnin Johannesburg ya ce “Kamfanin jiragen sama na Air Peace zai fara jigilar mutanen ranar Laraba inda jirgin farko zai dauko mutane 320. Zamu sake tashin karin wani jirgin babu jimawa bayan wannan.”

Buhari ya bayar da umarnin lokacin da ya karbi rahoton, Ahmad Rufa’i shugaban hukumar leken asiri ta Najeriya wanda shine manzo na musamman da ya tura kasar ta Afrika ta kudu.


Like it? Share with your friends!

1
97 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like