Afrika: Ma’aikatar haraji ta Nijar da Kamfanin sadarwa na Orange sun cimma matsaya


Bayanin da shafin actuniger ya rawaito na cewa bangarorin biyu sun fahimci juna inda kamfanin na Orange zai biya rabin kudaden da ake binsa na haraji, daga bisani kuma ya dinga biya kadan-kadan.

Tuni dai aka bada umurnin bude babban ofsihin kamfanin na Orange, tare da kawo karshen matakin shari’a kan babban darektan kamfanin.

An dai jima ana ta kai ruwa rana tsakanin ma’aikatar harajin ta NIjar da kuma kamfanin mallakin kasar Faransa, wanda har ma kwanan baya aka fitar da sammacin hana shugaban kamfanin fita daga kasar.


Like it? Share with your friends!

-1
99 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like