Afirka ta Kudu ta bawa Najeriya hakuri


Shugaban kasar Afrika ta Kudu,Cyril Ramaphosa ya bawa Najeriya hakuri kan hare-haren da aka kai wa yan Najeriya a kasar sa.

Jeff Radebe jakada na musamman daga kasar Afrika ta Kudu shine ya bawa shugaban kasa Buhari hakuri a madadin gwamnati da kuma al’ummar kasar Afrika ta Kudu lokacin da ya gana da shugaban a fadar Aso Rock ranar Litinin.

Ya ce kasar Afrika ta Kudu wani bangare ne na nahiyar Afirka da ta yarda da zaman lafiya da cigaban nahiyar.

Jakadan na musamman ya ce mutane 10 aka kashe a hare-haren, biyu daga ciki sun fito daga kasar Zimbabwe takwas kuma yan kasar Afrika ta Kudu.

Ya kara da cewa kasar Afrika ta Kudu za ta cigaba da nuna godiya ga Najeriya kan rawar da Najeriya ta taka wajen kawo karshen mulkin wariyar launin fata.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like