Ana wannan zaman kotu ne ta kafar bidiyo, sai dai lauyan da ke kare tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya nemi a dage zaman, domin ya samu damar halartar kotun a nan gaba. Duka wannan na zuwa ne bayan da Zuma ya kwashe sama da mako guda a gidan yari bisa laifin raina kotu da ya yi, lamarin da ya janyo gagarumar tarzoma a kasar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 da jikkata wasu da dama, baya ga kone gine-ginen gwamnati da na al’umma gami da wasoson dukiya.