Gwamnatin Afirka ta Kudu ta tura da karin dakaru dubu 25 domin taimaka wa ‘yan sanda kwantar da tarzomar da ta barke a yankin Kwazulu Natal, bayan matakin da hukumomin shari’a suka dauka na daure tsohon shugaban kasa Jacob Zuma bisa laifin raina kotu. Tun dai bayan tisa keyar tsohon shugaban gidan yari ne rikicin da ya kunno kai ya rikide zuwa kone-kone da fasa shagunan mutane domin kwasar ganima. 

 Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin Afirka ta Kudu ta tura da adadin sojojin mai yawa, tun bayan rikicin kawo karshen wariyar launin fata a shekarar 1994. A halin yanzu ma, wasu dakarun dubu 14 na zaman jiran ko ta kwana domin bazama inda ake tashin hankali da nufin yin fito na fito da masu tarzoma.

Yankin Gautend da ke zama mafi girma, kuma daya daga cikin masu yawan al’umma na daga cikin wuraren da aka tura jami’an sojin. 
Tun bayan barkewar rikicin an yi nasarar danke sama da mutane dubu yayin da wasu 72 suka rigamu gidan gaskiya.