Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani da iyalinsa suna cikin koshin lafiya a Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar yadda wata sanarwa da Daular Larabawar ta fitar ta fadi. An kwashi kwanaki ba tare da jin duriyarsa ba, bayan da shugaban ya tsere daga kasar a yayin da turar mayakan Taliban ta kai shi bango. A jawabinsa na farko tun bayan da ya nemi mafaka, Shugaba Ghani ya ce, ya dauki matakin barin kasar don hana aukuwar bala’in da zai janyo zubar da jini, musanman na fararen hula.

A ranar 15 ga wannan watan na Agusta da muke ciki, ya tsere a lokacin da mayakan Taliban suka soma samun galaba a karbe ikon kasar. Yayi mulkinsa na tsawon shekaru bakwai, na wa’adi biyu a jere, bayan da ya lashe zaben kasar bisa tsarin mulkin demokradiya. Kafin ma zama shugaban kasa, Ashraf Ghani ya rike mukamin ministan kudi, ana kuma yaba masa kan rawar da ya taka a farfado da tattalin arzikin kasar da ya ragargaje bayan faduwar gwamnatin Taliban na wancan lokacin.