Harin wanda tuni da kungiyar IS ta yi ikirarin daukar alhakinsa, ya rutsa da jama’ar a kasuwar Sadr City wata unguwa ta ‘yan Shi’a a lokacin da suke yin cefane na bikin sallah. Masu aiko da rahotanin sun ce an rika ganin sassan jikin mutane a a ci-cire a kasa mata da maza da ma yara, kuma shaguna da kantina  na ci da wuta. Wannan shi ne hari na biyu na kunar bakin wake da ‘yan ta’ddar ke kai wa a Bagadaza tun farkon wannan shekara.