AFCON: Koulibaly ya mayar wa Napoli martani | Labarai | DWDan wasan baya a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Kalidou Koulibaly, ya yi kira ga mamallakin tsohon kulob dinsa na Napoli ta lig din Serie A na Italiya da ya mutunta kungiyoyin kwallon kafa na Afirka, a daidai lokacin da furucin jami’in na Napoli ke ci gaba da fusata ‘yan kwallon kafar Afirka da ke Turai.

A ranar Talata ce dai aka ruwaito  Aurelio De Laurentiis na cewa daga yanzu ba zai sanya hannu a kwantaragi da wani dan kwallo na Afirka ba, har sai dan wasan ya amince a rubuce cewa ba zai shiga gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON ba. Mai kulob din Napolin, ya ce ya lura a duk lokacin da aka zo gasar AFCON ba ya samun hankalin ‘yan wasansa na Afirka. 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg