Adeyeye ya fice daga jam’iyyar PDP


Dayo Adeyeye, mai neman zama dantakarar gwamnan jihar Ekiti karkashin jam’iyar PDP ya fice daga jam’iyar inda ya ce ya shirya komawa wata jam’iyar.

Adeyeye wanda ya samu kuri’a 771 cikin kuri’a 1986 da aka kada a zaben fidda gwanin jam’iyar da aka yi, ya bayyana matakin nasa ne ranar Alhamis a Ado Ekiti babban birnin jihar.

Toshon karamin ministan ayyukan ya ce zai sanar da sabuwar jam’iyyar da zai koma cikin awanni 48 inda ya ce jam’iyyu da basu gaza biyar ba sun yi masa tayin tsayawa takarar karkashinsu na zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 14 ga watan Yuli.

Toshon kakakin jam’iyar PDP ya yi wannan sanarwa ne jim kadan bayan da ya tuntubi magoya bayansa kan matakin da za su dauka anan gaba biyo bayan rashin nasarar da yayi a hannun Kolapo Olusola-Eleka wanda shine mataimakin gwamnan jihar Ayodele Fayose.

Ya yi zargin cewa nasarar da olusola ya samu tamkar cigaban mulkin Ayo Fayose ne.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like