Addini: Falalar Daren Lailatul Qadr A Watan Ramadan Ana sa ran ganin daren nan mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan. Babu shakka daren Laylatul Qadr na nan cikin kwanaki goma na karshe. 

Ibada a wannan dare dai tana gaba da ibadar shekaru akalla 84. Daren Lailatul Qadr na da Falalar gaske. 
Manzon Allah SAW ya tabbatar da cewa za a dace da daren nan na Laylatul Qadr mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan na 10 na karshen watan Ramadan inda ake kasafin duk wani alheri a shekarar. 

Ibada a cikin daren kamar yadda ya zo a Al-kur’ani cikin Suratul Qadr ya zarce ibada har na watanni dubu wanda idan aka lissafa zai bada kusan shekaru 84.

Manzon Allah ya nemi a lalubi daren a cikin kwanaki na mara watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma daren azumi na 29.

Haka kuma yayin da ake azumin watan Ramadan yana daga cikin ayyukan lada shiga I’itikafi watau kebawa a Masallaci ba a wani aiki face salloli da karatun Al-kur’ani mai girma a wannan lokaci.

Comments 0

Your email address will not be published.

Addini: Falalar Daren Lailatul Qadr A Watan Ramadan 

log in

reset password

Back to
log in