Adam A Zango Ya Saki Hotunan da Suka Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa Adam Zango ya sake jawo wa kansa abin fada bayan a kwanakin baya ya yi rantsuwa da Al’kurani mai girma a wata kafar sadarwar talabijin cewa shi ba dan luwadi ba ne kuma ya fitar da wata budaddiyar wasika zuwa ga abokan adawarsa da ya ke zargi suna dangantashi da harkar luwadi.

A wannan sabuwar shekarar jarumin ya fitar da wasu hotuna guda bakwai da suka jawo cece-kuce inda biyar daga cikin hotunan yana rungume da matarsa Ummukulsum suna yi wa junansu dariya sauran biyun kuma hoton Ummukulsum ne ita kadai. 

Matar tasa Ummukulsum ‘yar asalin kasar Kamaru tana da diya daya da jarumin fina finan wadda aka haifa a ranar 31 ga watan Janairun shekarar da ta gabata. 

A hotunan da jarumin ya fitar rungume da matarsa cikin annashuwa ya yi wa kowanne rubutu a kasansa inda ya nuna irin son da ya ke yi wa matar tasa, hoto na farko ya rubuta kamar haka, “Fulawa ba ta kai ki kyawu ba, taurari ba su kai ki haske ba, rayuwa ba za ta yi dadi idan babu ke”.
Hoto na gaba da Arewa24news ta samu, jarumin ya rubuta kamar haka “soyayya na cikin yana yanayi inda ina jinsa kuma ina ganinsa duk domin ke, tabbas na yi sa’a da na same ki mai kaunata kuma matata.”
Jarumin ya rubata a hoto na gaba “matata abar alfaharina a kullum ke nake gani a kusa da ni idan na tashi, rayuwa tana yi mani kyau a duk lokacin dana farka na fara da ganinki.”

Zango ya yi rubutun baitoci soyayya da yabo ga matar tasa a sauran hotunan daya dora a kafar sadarwa ta Instagram inda ya sha Raddi ga masu bibiyarsa har sama da 1,500.

Zango ake zaginsa da auri saki masu bibiyarsa sun bayyana Ummukulsum a matsayin ita ce matarsa ta biyar a jerin sunayen matan daya aura tun daga kan uwar gidansa Aisha da ya aura suka hayayyafa wadda yanzu haka sun rabu da jarumin watanni takwas da su ka wuce inda ta koma garinsu Shika.

Daga cikin masu bayyana ra’ayinsu a hotunan da jarumin ya dora wani yace hotunan nan basu dace anan ba matarka matarkace kai kadai dan haka ku rika rufe sirrinku tsakaninku. 

Zango dai ya sha martani kala-kala gameda Hotunan daya dora ya bayyana ta bakin wani nakusa da shi cewa wannan ba shi ne karo na farko da jarumin ya dora hotonsa dana matarsa ba.


Like it? Share with your friends!

-9
98 shares, -9 points

Comments 14

Your email address will not be published.

  1. kaii jama’a!!! shi wai zango me yayiwa mutane haka ne, duk irin hotunan da mutane sukeyi kapin suyi aure ba’a cewa komai sai shi dan yayi da matarsa??? wanda to sukeyi da matan da basu auraba su me yasa bakwa magana akansu??? haba kullun zango zango zango…. duk ga yan iska nan a gari amma duk bakwa maganarsu.. haba dan Allah

  2. Ikon Allah sai kallo, wannan pha matarsa ce, dan yayi wannan hotunan da matarsa shine laipi ko?? to a barshi a laifi ne,, to wannan hotunan da mutane kuma sukeyi kapin aure kaga na miji bai auri mace ba amma kaga ra rungumeta, su me yasa bakwa cewa komai a kansu??? haba jama’a ku dinga yiwa mutane adalci mana, kaga mutum ya jawo yarinya jikinsa ya matse, kuma ba aure a tsakaninsu amma shiru kake ji.. Amma kana hawa internet zango zango zango……. to wlh zango dai sai ta Allah ba ta mutun ba

    1. Dama duk wanda yake tunanin yan film ba yan iska bane to wlh shima dan iskane saboda wlh duk yan film yan iskane wai su suce fadakarwa ko wa azzantarwa to wlh kuskure suke yi dan haka jama ku kiyaye suma in basu gyara ba wlh insuka mutu wlh azaba za.amusu daga ni (isah yahaya UDUBO GAMAWA LOCAL GOVERMENT)

  3. Dama masu cewa yan film ba yan iska bane ai suma yan iskane saboda wlh yan film sabon allah suke yi wai sai suce fadakarwa wa.azantarwa to wlh in basu tuba ba wlh allah zai musu azaba dan haka ku tuba kafin ku koma zuwaga Allah daga (isah yahaya UDUBO GAMAWA LOCAL GOVERMEN)

  4. Hmmm Allah ya Kyauta ! Manzon Allah ya ce “Wanda ba ya kishin iyalinsa ba zai shiga Aljanna ba” Allah ya shirye mu baki daya.

  5. Write a comment *en uwa musulmai yakamata mubar sa ido akan abunda bai shafemuba koyayima ai matansane allah yashiryemu baki daya

You may also like